Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya taya tsohon shugaba Muhammadu Buhari murnar cika shekaru 82 a duniya.
Atiku ya yi fatali da bambancin akidar siyasa yayin da ya rubuta samon taya murnar.
Tsohon dan takarar shugaban kasar ya kuma yi addu’o’i na samun karin ingancin lafiya da kwanciyar hankali ga Buhari.
A madadin iyalina, ina taya tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, @MBuhari, murna a ranar zagayowar haihuwarsa ta 82. Ina rokon Allah Madaukakin Sarki ya ci gaba da ba ka karin shekaru cikin koshin lafiya da kuzari. – AA
Atiku ya aika sakon addu’o’i ga tsohon shugaban kasa Buhari