Tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan ya taya tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari murnar cika shekaru 82, yana masa fatan lafiya da kwanciyar hankali.
A cikin sakon taya murnar da ya fitar a ranar Litinin a Abuja, Jonathan ya yaba da rawar da Buhari ya taka wajen hada kan kasa da bunkasa cigaban Najeriya.
Ya kuma jaddada godiyarsa ga jajircewar Buhari wajen samar da ci gaba da dorewar Najeriya.
Jonathan yayi addu’ar Allah ya karawa Buhari lafiya, hikima, da farin ciki.
Jonathan ya taya tsohon Shugaban Kasa Buhari murnar cika shekaru 82