in

Akpabio ya nemi Tinubu ya tsawatarwa Ministoci

Shugaban majalisar dattawan Najeriya, Godswill Akpabio, ya yi kira ga shugaban ƙasa, Bola Tinubu, da ya ɗauki mataki kan ministocin da ke ƙin amsa gayyatar majalisar dokoki.

A cewarsa, irin waɗannan ministocin masu nuna halin ko-in-kula ba su cancanci zama a cikin gwamnatinsa ba.

Akpabio ya bayyana wannan ra’ayin ne a ranar Laraba yayin gabatar da kasafin kuɗin 2025 da shugaban ƙasa ya yi.

“Waɗanda ba sa amsa gayyatar majalisar dokoki ba ƴan siyasa ne na gaskiya ba, don haka bai dace su samu gurbi a gwamnatinka ba,” in ji Akpabio ga Tinubu.

Akpabio ya nemi Tinubu ya tsawatarwa Ministoci

Tallafin kuɗin wutar lantarki ya karu zuwa N199.64bn – NERC

Cyclone Chido death toll in Mozambique rises to 45