in

An kama mutane 2 a Gombe da laifin kokarin siyan wake da kudin bogi

An kama wasu mutune biyu, Garba Audu da Kabiru Abubakar, mazauna unguwar Laying Arfa a Gombe, bisa laifin kokarin siyan buhunan wake da kudin bogi.

Wanda abin ya shafa, Idris Usman, ya bayyana cewa mutanen sun tsaida shi a hanyarsa zuwa kasuwar Lariski, inda suka yi ciniki na buhunan wake biyu akan Naira 210,000. Amma bayan ya gano cewa kudin bogi ne, yayi ihu wanda ya sa aka kama su.

Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Gombe, ASP Buhari Abdullahi, ya gabatar da wadanda ake zargi a ranar Talata.

Ya bayyana cewa yayin bincike, mutanan sun amsa laifinsu, inda suka ce sun samo kudin bogin ne daga wani Abdullahi mai lakabin “Manci” daga karamar hukumar Potiskum a Jihar Yobe, wanda yanzu haka yana tsere.

“Mun kama wadanda ake zargi, sannan muka bincika motarsu. Mun gano buhunan wake biyu da kuma N39,000 da ake zargin kudin bogi ne,” in ji ASP Buhari Abdullahi.

Kakakin ya tabbatar da cewa za a gurfanar da wadanda ake zargin a kotu bayan kammala bincike.

Hakazalika, ya gode wa jama’a bisa hadin kansu da kuma bayar da bayanai masu muhimmanci da suka taimaka wajen kama wadanda ake zargi.

“Mun gode wa jama’a bisa tsare-tsaren su da saurin daukar mataki kan wannan al’amari,” in ji shi.

An kama mutane 2 a Gombe da laifin kokarin siyan wake da kudin bogi

Beyoncé becomes most RIAA certified female artist of all time

Naira scarcity: CBN fixes N100,000 as limit for PoS withdrawal