An ware naira tiriliyan N15.81 domin biyan kudin ruwan bashi a cikin kudirin kasafin kudi na 2025 da Shugaban kasa Bola Tinubu ya gabatar wa mjalisar dokoki ta kasa.
Kasafin kudin na naira tiriliyan N47.9, wanda aka gabatar a ranar Laraba, ya ba da fifiko ga fannin tsaro wanda ya samu kaso mafi girman kaso.
Shugaban ya bayyana cewa an ware naira tiriliyan N4.91 ga tsaro da naira tiriliyan N4.06 ga ayyukan gine-gine, naira tiriliyan N2.4 ga bangaren Lafiya, yayin da bangaren Ilimi ya samu naira tiriliyan N3.5.
Hakazalika, shugaban ya ce an yi hasashen samun kudin shiga na naira tiriliyan N34.8, an kuma yi hasashen raguwar hauhawar farashi daga kashi 34.3% zuwa kashi 15%.
An ware Naira Tiriliyan N15.81 don biyan kudin ruwan bashi a kasafin kudin 2025