Wasu bata gari sun yi kutse a shafin Intanet na gukumar kididdiga ta kasa (NBS).
Jaridar The Guardian ce ta gano haka a daren Laraba kafin hukumar ta tabbatar da lamarin.
Hukumar NBS ta tabbatar da lamarin a cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafin X.
A sanarwar, NBS ta bukaci ‘yan Najeriya su yi watsi da duk wani saƙo ko rahoto da aka wallafa a shafin har sai an kammala mayar da shi yadda ya kamata.
“Muna sanar da jama’a cewa an yi kutse a shafin intanet na NBS, kuma muna kan kokarin dawo da shi. Don haka, ku yi watsi da duk wani saƙo ko rahoto da aka wallafa har sai shafin ya dawo ya daidai. Mun gode.”
Sai dai hukumar ta kasa bayyana wa’adin da za a gyara shafin da kuma lokacin da zai koma aiki yadda ya kamata.
Wannan lamarin ya faru ne wasu makonni bayan NBS ta fitar da muhimman bayanai da su ka shafi tsaro a cikin shekarar 2024 a Najeriya.
An yi kutse a shafin intanet na NBS