in

Gwamnan Kebbi ya kaddamar da kasafin kudin sama da N580b

Gwamnan jihar Kebbi, Dr. Nasir Idris, ya gabatar da kasafin kudin shekarar 2025 mai kimanin Naira biliyan 580.33 ji

A cewar Gwamnan, an sanya wa kasafin sunan “Karuwar tattalin arziki da Inganta abubuwan more rayuwa”.

Dr. Idris ya bayyana cewa, za a samu kudaden gudanar da kasafin kudin daga wurare daban-daban, ciki har da kudaden shiga na cikin gida da aka kiyasta zai kai kimanin Naira biliyan 25.98.

Ya ce, jimillar kudaden gudanarwa na shekarar sun kai Naira biliyan 127.4, wanda ya hada da kudaden albashi na Naira biliyan 57.93 da kuma kudaden gudanar da ayyuka na sama da Naira biliyan 70.21.

A daya bangaren kuma, gwamnan ya ce kudaden manyan ayyuka za su kai sama da Naira biliyan 453.18.

Dr. Idris ya bayyana cewa, kasafin kudin zai tabbatar da saukaka harkokin kasuwanci ta hanyar inganta muhimman tsare-tsare da ka’idojin tattalin arziki.

Haka kuma, ya ce kasafin zai kawo sauye-sauye a bangaren shari’a domin kara karfafa tsaro da kuma jawo hankalin masu zuba jari daga cikin gida da da waje.

Ya kara da cewa, kasafin zai ci gaba da tabbatar da gudanar da ayyukan ci gaban birane da kauyuka domin kara inganta rayuwar al’ummar jihar.

A cewarsa, kasafin kudin shekarar 2025 zai samar da damammaki da dama ga al’ummar jihar duk da kalubalen da ake fuskanta.

Ya ce kasafin kudin zai inganta sauye-sauyen tsare-tsare masu nagarta, bisa ka’idar gaskiya, rikon amana da bin doka.

Gwamnan ya kuma ce za a ci gaba da hada kai don inganta shugabanci da samar da ingantattun ayyukan jin dadi ga al’umma.

Daga cikin manyan tsare-tsare, gwamnan ya ce za a kara inganta tsaro, bunkasa aikin noma, da kuma karfafa hakar ma’adanai ta hanyar amfani da fasaha.

Ya kuma ce gwamnatinsa za ta kara zage dantse don ganin tattalin arzikin jihar ya ci gaba duk da matsalolin da suka biyo bayan cire tallafin mai.

Gwamnan ya kara jaddada cewa an sanya aikin gyaran hanyar Koko-Mahuta a kasafin kudin, kuma nan ba da jimawa ba za a fara aikin.

Ya kuma bayyana farin cikinsa cewa kasafin kudin shekarar 2024 ya taimaka wajen cika alkawuran kamfen dinsa, wanda ya haifar da gagarumin sauyi a bangaren ababen more rayuwa, tare da alkawarin ci gaba da wannan yanayi a shekarar 2025.

Ya yaba da kyakkyawar dangantaka tsakanin bangarorin gwamnati biyu, wato bangaren zartarwa da na majalisa, yana mai jinjinawa majalisar dokokin jihar kan goyon bayanta.

Gwamnan Kebbi ya kaddamar da kasafin kudin sama da N580b

‘Friend of the Poor’ – Femi Adesina reveals why Buhari did not remove fuel subsidy

‘Opposition behind resurgence of violence in Kano’ – Gov Yusuf