Gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke ya bayar da umarnin gudanar da bincike cikin gaggawa kan shari’ar wani Segun Olowookere da aka yankewa hukuncin kisa akan laifin satar kaza.
Gwamna Adeleke ya ba da wannan umarnin ne ta wata sanarwa da mai magana da yawun sa Olawale Rasheed ya fitar a ranar Talata.
Gwamnan ya umurci babban mai shari’a na jihar da ya sanya mutumin a jerin wadanda za ayiwa afuwa kafin karshen shekarar nan.
Umurnin dai na zuwa ne bayan wani roko na jin kai ga gwamnan a madadin Segun Olowookere da cibiyar zaman lafiya ta duniya ta yi.
Babban darakta na cibiyar, Lamina Kamiludeen Omotoyosi, ta bayyana cewa Olowookere an yanke masa hukuncin kisa ne shekaru 10 da suka gabata yana da shekaru 17 a duniya.
Omotoyosi ta ce, “Hukuncin Segun ya samo asali ne daga wani abin da ya faru da ya hada da zargin satar kaza da ƙwai a wata gona a Oyan, jihar Osun sama da shekaru goma da suka wuce.”
Tace hukuncin kisan da aka yanke masa yayi tsauri la’akari da lefin daya aikata da karancin shekarunsa hakan yasa suka bukaci gwamnatin ta shiga lamarin ta bincike tangardar da aka samu a shari’ar tare da tabbatar da anyi masa adalci.
Gwamnan Osun ya bukaci a binciki hukuncin kisan da aka yankewa wani matashi daya saci kaza