in

Gwamnati bata da hurumin cigaba da tsare Nnamdi Kanu – Ohanaeze

Shugaban kungiyar Ohanaeze Ndigbo, Nze Ozichukwu Fidelis Chukwu, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ba ta da isasshen dalili na ci gaba da tsare Nnamdi Kanu, jagoran kungiyar IPOB.

A wata sanarwa da kakakin Ohanaeze, Alex Ogbonnia, ya fitar, Shugaban kungiyar ya jaddada cewa “ba wani dalili mai gamsarwa da zai sa a ci gaba da tsare Kanu na tsawon lokaci da jami’an tsaro suka yi.”

Chukwu ya tabbatar wa kwamitin zartarwa na kasa (NEC) cewa za su samar da wani tsari na musamman da zai tabbatar da cewa Ohanaeze tana karfafa kyakkyawar niyya da manufofin gwamnati, tare da shawo kan kalubale da ka iya tasowa.

Ya kara da cewa duk da kwanakin sa a ofis sun kusa karewa, yana da karfin gwiwa cewa zai bar kyakkyawan tarihi a kungiyar.

Gwamnati bata da hurumin cigaba da tsare Nnamdi Kanu – Ohanaeze

War: Ukraine assassinates Russia’s head of chemical weapons, Kirillov

Jigawa court sentences two kidnappers to death for abduction, murder