Sabon kwamishinan ma’aikatar sanya ido da kula da ayyukan da gwamnatin Kano ke gudanarwa Injiniya Ibrahim Muhammad Diggol ya sha alwashin fito da sabbin tsare-tsaren da zasu tabbatar ganin ana aiwatar da dukkan kudurorin gwamnati yadda ta tsara su.
Diggol ya bayyana hakan ne lokacin da yake karbar ragamar tafiyar da ma’aikatar daga tsohon shugaban ta Ali Namadi Dala, yayi alkawarin bude kofar sa domin gudanar da aikin da al’ummar kano zasu amfana.
Injiniya Diggol wanda shine tsohon kwamishinan Ma’aikatar Sufuri ta jihar nan yace a lokacin da yake jan ragamar ma’aikatar Sufurin ansamu cigaba matuka a bangaren sufurin jihar nan musamman a fannin habaka tattalin arziki, tare da gyara motocin safa-safa domin daukar dalibai zuwa makaranta baya ga samar da rigar kariya daga nutsewa a ruwa ga kananan hukumomin da suke amfani da hanyar sufuri ta ruwa.
Jam’in yada labaran ma’aikatar Sufurin ta Kano Ibrahim Adamu Kofar Nassarawa ya rawaito tsohon kwamishinan ma’aikatar ta sanya ido da kula da ayyukan da gwamnatin Kano ke gudanarwa Alhaji Ali Namadi Dala wanda yanzu ya koma ma’aikatar Sufurin jihar nan, yace zai yi aiki tukuru domin sauke nauyin da gwamna Abba Kabir Yusif ya dora masa.
Namadi ya bukaci ma’aikatan dake ma’aikatar sanya ido da kula da ayyukan da gwamnatin Kano ke gudanarwa dasu bawa sabon kwamishinan cikakken hadin kai da goyon baya domin ciyar da jihar Kano gaba.
Sabon kwamishinan Kano ya sha alwashin tabbatar da muradun gwamnatin Abba