Hukumar kula da wutar lantarki ta Najeriya (NERC) ta bayyana cewa kuɗin tallafin lantarki da gwamnatin tarayya ke bayarwa.
Hukumar ta bayyana cewa kudin ya tashi zuwa Naira biliyan 199.64 a watan Disamba 2024.
Wannan ya fito daga wani rahoto da hukumar ta fitar, kamar yadda tashar Channels ta ruwaito.
Rahoton ya nuna cewa tallafin ya ƙaru da 2.76%, daga Naira biliyan 194.26 da aka rubuta a watan Nuwamba, zuwa Naira biliyan 199.64 a watan Disamba.
Hukumar NERC ta bayyana cewa wannan ƙarin ya samo asali ne daga faɗuwar darajar Naira, inda darajar dala ta kai naira 1,687.45 kamar yadda aka ƙiyasta a kasafin kuɗi, tare da hauhawar farashin kayayyaki wanda ya kai kashi 33.9.
Rahoton ya nuna cewa gwamnatin tarayya ba ta sauya farashin wutar lantarki ba a wannan lokacin.
Tallafin kuɗin wutar lantarki ya karu zuwa N199.64bn – NERC