in

Yara da dama sun mutu a wani turmutsutsu a birnin Ibadan

Yara kanana da dama sun rasa rayukansu a wani mummunan turmutsutsu da ya faru a wani bikin al’adu da aka gudanar a Ibadan, babban birnin jihar Oyo.

Lamarin ya faru ne a unguwar Bashorun da ke Ibadan a ranar Laraba.

Ba a tabbatar da yawan wadanda suka mutu ba a lokacin da aka hada wannan rahoton.

Sai dai an samu labarin cewa an garzaya da wadanda suka jikkata zuwa wasu asibitoci a cikin birnin Ibadan.

Rahotanni sun ce duk da an shirya gudanar da bikin ranar Laraba, amma tun Talata wasu iyaye suka kai yaransu wajen, yayin da wasu suka iso wajen da sanyin safiyar Laraba.

Cunkoson shiga wajen ne ya haifar da turmutsutsun, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar yara da dama.

Yunkurin da DAILY POST ta yi don jin ta bakin jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Oyo, Adewale Osifeso, bai yi nasara ba.

Amma dai, gwamnatin jihar Oyo ta tabbatar da aukuwar lamarin cikin wata sanarwa.

Kwamishinan labarai da Wayar da Kai, Dotun Oyelade, bayan tabbatar da lamarin, ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta dauki matakin gaggawa.

“Gwamnatin Jihar ta hanzarta tura jami’an ceto da daukin gaggawa bayan samun labarin faruwar lamarin.

 

Yara da dama sun mutu a wani turmutsutsu a birnin Ibadan

NSCDC deploys 1,800 officials ahead of Yuletide in Ondo

An ware Naira Tiriliyan N15.81 don biyan kudin ruwan bashi a kasafin kudin 2025