Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya musanta zargin kwace fili mallaminsa a Abuja, kamar yadda labarai ke cewa ministan Abuja Nyesom Wike ya kwace wasu daga cikin filayen Buharin saboda rashin biyan haraji.
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai Magana da yawunsa Garba Shehu ya fitar a yammacin Alhamis.
Garba Shehu yace “Ba Buhari kansa ba ne ke da mallakar wannan fili da aka ce an kwace ba, an ware filin ne da sunan “Muhammadu Buhari Foundation.” Wata Gidauniya, wadda wasu mutane dake kusa dashi suka kafa, kuma a iya sani na sun gudanar da komai cikin doka”
Sai dai sanarwar tace gidauniyar ta gamu da cikas bayan da sashen kas ana birnin tarayya ya kakaba mata kudin da ba zata iya biya ba, domin mallakar takardar shaida, wanda ya zarce abinda sauran kungiyoyi suka saba biya.
Shehu yaya zargin cewa anyi hakan ne da gangan, amma ba kuskuren ba,
“A matsayinsa na mutum, tsohon shugaban ƙasa yana da fili a Abuja da sunansa. Lokacin da aka gayyace shi da sauran ministocinsa don cike fom ɗin neman fili a lokacin mulkinsa, ya mayar da fom ɗin ba tare da cikewa ba, yana cewa tuni yana da fili a Abuja, kuma waɗanda ba su da shi ne za a ba su. Saboda haka, ya ƙi amincewa da tayin.
Ba filin Buhari aka kwace ba-Garba Shehu