Wasu bama-bama da ake zargin ‘yan bindiga sun dasa sun tashi a yankin Bassa, karamar hukumar Shiroro ta jihar Neja.
Bama-bamai sun kashe kashe yaro guda, sannan wasu mutane hudu sun rasa kafafunsu.
Tuni aka binne wanda ya rasu, yayin da sauran yaran da suka ji rauni ke karbar magani a Asibitin Kwararru na IBB, Minna.
Lamarin ya faru ne ranar Alhamis lokacin da yaran suka tsinci bama-bamar a kasa suna wasa da ita, inda ta tashi nan take ta kashe daya daga cikinsu a wurin sannan ta raunata sauran.
Wani mazaunin yankin, Ahmed Almustapha, ya bayyana cewa uku daga cikin yaran da suka ji rauni ‘yan uwansa ne.
Ya ce wannan shi ne karo na biyu da irin wannan fashewa ta faru a Bassa cikin wata guda, inda ta yi sanadin mutuwar mutum daya a makon da ya gabata lokacin da yake kan hanyarsa ta zuwa gona.
Ya yi kira ga gwamnatin jihar Niger da ta tarayya da su kawo musu dauki domin su samu damar komawa gonakinsu.
Kwamishiniyar Sufuri ta jihar, Hadiza Kuta, ta tabbatar da lamarin, tana mai bayyana cewa wannan lamari ya kasance abin bakin ciki sosai.
Bam ya tashi da yaro a jihar Niger, wasu sun ji munanan raunuka