Hukumar Tsaro ta Civil Defence ta Najeriya, reshen Babban Birnin Tarayya, ta tabbatar wa da mazauna da za a samar da isasshen tsaro a lokacin bukukuwan Kirsimeti da Sabuwar Shekara.
Kwamandan reshen FCT, Olusola Odumosu, ya bayyana cewa an tura jami’ai 4,000 fadin Abuja, FCT da kewayenta domin kiyaye rayuka da kare muhimman kadarorin kasa da ababen more rayuwa.
Odumosu, a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, Monica Ojobi, ta sanya hannu kuma ta fitar a ranar Alhamis, ya umarci jami’an su tabbatar da bin umarnin aikin da aka bayar.
Ya gargadi wadanda ke shirin amfani da lokacin bukukuwan don aikata laifuka cewa zasu fuskanci mummunan hukunci, inda ya bayyana cewa rundunar ta shirya tsaf domin dakile duk wata barazana ga tsaro.
Bikin Kirsimeti: NSCDC ta tura jami’ai 4,000 FCT