in

EFCC tayi sammacin shugabannin kananan hukumomin da aka sauke a jihar Edo

Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ta gayyaci shugabannin kananan hukumomi 18 da aka dakatar a Jihar Edo zuwa ofishinta don gudanar da bincike.

Takrdar gayyatar da daraktan Bincike na EFCC, Abdulkarim Chukkol ya rubuta, an aika ta ne ga sakataren gwamnatin Jihar.

A cikin wasikar mai kwanan watan 17 ga Disamba, Chukkol ya umarci shugabannin kananan hukumomi na Akoko-Edo, Egor, Esan Central, Esan North East, Esan South East, da Esan West da su zo ofishin EFCC a ranar Alhamis, 19 ga Disamba.

Sauran shugabannin da ake sa ran su zo a ranar Alhamis sun hada da na Etsako Central, Etsako East, da Etsako West.

Shugabannin sauran kananan hukumomi na Igueben, Ikpoba Okha, Orhionmwon, Ovia North East, Ovia South West, Owan East, Owan West, da Uhunmwode suna cikin jadawalin wadnda zasu je ofishin EFCC din ranar Jumma’a, 20 ga Disamba.

Daraktan binciken ya bukaci shugabannin da su kawo kwafin takardun shaida na cikakken bayanin ma’aikata da kuma albashinsu.

Har ila yau, an nemi cikakkun bayanai game da asusun da ake karɓar kudaden albashi daga gare su, bayanin asusun da ake ajiye kudaden albashi na gaggawa, da kuma bayanan asusun daga ranar 1 ga Janairu har zuwa yanzu.

EFCC tayi sammacin shugabannin kananan hukumomin da aka sauke a jihar Edo

Bam ya tashi da yaro a jihar Niger, wasu sun ji munanan raunuka

Mutane 35 ne suka mutu a turmutsutsun birnin Ibadan