Gwamnatin Jihar Ekiti ta nemi al’ummar jihar da suyi watsi da jita-jitar da ake yadawa game da tallafin kudin N25,000 na Kirsimeti da ake zargin Gwamna Biodun Oyebanji na rabawa.
A cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Alhamis, Mai ba Gwamna shawara kan Harkokin Media, Yinka Oyebode, ya bayyana wannan labarin a matsayin wanda ba shi da tushe kuma yayi gargadi ga jama’a kan kauce wa fadawa cikin shiryayyun hanyar damfara.
Sanarwar ta ce: “Muna sanar da jama’a cewa bayanin da ake yadawa game da tallafin kudi na N25,000 na Kirsimeti daga Gwamnan Jihar Ekiti, Mista Biodun Oyebanji, karya ne kuma ya kamata a yi watsi da shi.
“Gwamnan baya gudanar da kowanne irin tallafin kudi ko rarraba kudi ta hanyoyin da basu dace ba ko kuma ta dandamali na kan layi.”
“Mun roki al’ummar jihar dasu kasance a cikin shakka kuma kada su bayar da bayanan sirri ga shafukan yanar gizo ko mutane da ba a ba su izini ba, wadanda ke kokarin yaudararsu.”
Gwamnatin ta roki mazauna jihar su dogara ne kawai da tushen bayanai da aka tabbatar don samun sabbin labarai, domin kauce wa fada hannun masu zamba.
Gwamnatin Ekiti ta karyata jita-jitar N25,000 na kirsimeti