Jami’an tsaro sun kama fitaccen mawakin siyasa Malam Idris Dan Zaki Burum-Burum.
Mawakin ya yi wa Sanata Kawu Sumaila da Alhassan Ado Doguwa wakoki.
Rahotanni sun bayyana cewa, har yanzu ba a fayyace dalilin kama mawakin ba.
Amma ana zargin mama Burum-burum ba zai rasa nasaba da wata waka da ya yi inda aka yi zargin kalaman cin mutunci da ya yi wa jagoran Kwankwasiyya, Sanata Dr. Rabiu Musa Kwankwaso, da gwamnatin jihar Kano.
Ana zargi Dan Zaki da yin wasu kalaman batanci a cikin wakokinsa, inda ya yi wa wadanda gwamnatin Kano ta nada a mukamai shagube.
Jami’an tsaro sun kama mawakin siyasa, Idris dan zaki burum-burum