A ranar Alhamis ne babbar kotun birnin tarayya ta bayar da belin tsohon gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello a kan kudi naira miliyan 500 tare da mutane biyu da za su tsaya masa.
Da take yanke hukuncin, Mai shari’a Anenih ta amince cewa laifin da ake tuhumar wanda ake kara na 1 da shi abu ne da za a iya bayar da belinsa, sannan ta bayar da belin tsohon gwamnan a kan kudi Naira miliyan 500, tare da mutane uku da za su tsaya masa.
Tace “dole ne wadanda za a tantance su zama fitattun ‘yan Najeriya masu kadarorin kasa a Maitama, Jabi, Utako, Apo, Guzape, Garki, da Asokoro. An kuma umurci wanda ake kara na 1 da ya ajiye fasfo dinsa da sauran takardun tafiya kasar waje a gaban kotu”
Hakazalika mai shari’ar tace Yahaya Bello zai ci gaba da zama a gidan gyaran hali na Kuje har sai an cika sharuddan belin.
Kotu ta bayar da belin Yahaya Bello akan miliyan 50