Babbar kotun jihar Kano ta umarci gwamna, Abba Kabir Yusuf, ya biya kamfanin Lamash Properties, Naira biliyan takwas da miliyan dari biyar da goma sha daya a matsayin diyyar gine-ginen da ya rushe wa kamfanin a filin otal din Daula.
Kotun karkashin mai shari’a Sunusi Ma’aji, ta kuma umarci wadanda ake kara, gwamnatin jihar Kano, gwamna Abba Kabir da babban lauyan gwamnatin, su biya karin kudi Naira miliyan goma a matsayin kudin shigar da kara.
Kamfanin Lamash Properties ya shigar da kara kotun kan gine-ginen da aka rushe ba tare da wani dalilin doka ba, a watan Yunin 2023 bisa umarnin gwamna Abba.
Masu karar sun bayyana wa mai shari’a Ma’aji cewa, sun mallaki wannan fili ne ta hanyar yarjejeniya da gwamnatin Kano, karkashin mulkin Abdullahi Ganduje.
Lamash, ta hannun lauyansa Nureini Jimoh SAN, ya nemi kotu ta tabbatar da cewa yarjejeniyar da aka kulla tsakanin su da gwamnatin Kano don ayyukan kasuwanci a filin, tana nan daram kuma tana kan doka a lokacin da gwamna Abba ya rusa gine-ginen da ke filin.
A bangaren gwamnati, karkashin jagorancin lauyoyi Ibrahim Wangida da Bashir Muhammad, sun bayar da shaidar kare kansu, kamar yadda takardun kotu suka nuna.
Da ya ke yanke hukunci a jiya Laraba, mai shari’a Ma’aji ya amince da bukatun masu kara, inda ya tabbatar da cewa yarjejeniyar da aka kulla tana kan doka.
Ya ce an rushe gine-ginen ba bisa ka’ida ba, saboda haka ya umarci gwamnatin Kano ta biya diyyar kudin gine-ginen da ta rusa har Naira biliyan takwas da miliyan dari biyar da goma sha daya.
Idan za a iya tunawa dai, a watan Satumbar 2023, babbar kotun tarayya da ke nan Kano ta umarci gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta biya diyyar Naira biliyan talatin saboda rushe gine-ginen da ke filin idi na Kofar Mata.
A ranar Asabar, 3 ga Yunin 2023, kwana kalilan bayan rantsar da shi, gwamna Abba ya jagoranci tawagar rusau don rusa gine-ginen da ya yi zargin an yi ba bisa ka’ida ba a filayen gwamnati.
Kotu ta umarci gwamna Abba Kabir Yusuf ya biya diyyar 8.5bn kan rusa Daula otel ba bisa ka’ida ba