in

Kungiyar tsohon gwamna Shekarau ta fadi sharadin goyon bayan kudirorin haraji

Kungiyar farfado da dimokuraɗiyyar a Arewa (LND) ta gabatar da sharuɗɗan amincewa da dokokin gyaran harajin Shugaba Tinubu.

Da yake magana a wani taron jama’a da aka gudanar a Abuja, shugaban kungiyar kuma tsohon gwamnan Kano, Sanata Ibrahim Shekarau ya jaddada muhimmancin magance matsalolin da kwamiti da aka kafa don tantance kudurorin ya gano.

A cewarsa, binciken kwamitin ya nuna cewa akwai matsalolin zamantakewa, al’adu, da na shugabanci da za su iya haifar da babbar matsala idan aka yi watsi da su.

“Kungiyar LND na kallon ƙudurorin gyaran haraji a matsayin wata dama don bunƙasa zaman lafiyar tattalin arziƙin Najeriya tare da magance matsalolin kundin tsarin mulki, al’adu, da shugabanci,” inji shi.

Ya yi kira da a yi gyare-gyare sosai kan ƙudurorin domin tabbatar da adalci, bunƙasa hadin kan ƙsa, da kuma tabbatar da rarraba albarkatu bisa gaskiya da adalci.

Ana sa ran matsayar LND da shawarwarinta za su taka muhimmiyar rawa wajen tsara tattaunawar gyaran haraji da ake yi a majalisar tarayya.

Kungiyar tsohon gwamna Shekarau ta fadi sharadin goyon bayan kudirorin haraji

Serie A: Atalanta boss refuses to take credit for Lookman’s rise to stardom

Educate Nigerians on importance of tax reform bill – Christian group to FG