in

Mutane 35 ne suka mutu a turmutsutsun birnin Ibadan

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Oyo ta bayyana kama tsohuwar mai dakin Ooni na Ife, Naomi Silekunola, da shugaban makarantar Islamiyya ta Ibadan, Fasasi Abdulahi, da wasu mutane shida bisa mutuwar wasu yara yayin wani taro a Ibadan, babban birnin jihar, a ranar Laraba.

An ambaci tsohuwar sarauniyar a matsayin babbar mai tallafawa taron.

Haka kuma, adadin yara da suka mutu daga wannan mummunan lamarin ya karu zuwa 35 yayin da guda shida daga cikinsu suke cikin mawuyacin hali, kamar yadda wata sanarwa daga mai magana da yawun ‘yan sandan jihar, Adewale Osifeso, ya bayyana a ranar Alhamis.

Taron wanda aka gudanar a Makarantar Islamiyya ta Basorun, Ibadan, an tsara shi don yara 5,000, amma rahotanni sun nuna cewa adadin yaran da suka halarta ya zarce 7,500.

Osifeso ya bayyana cewa taron an shirya shi ne ta hanyar Wings Foundation, tare da hadin gwiwar gidan rediyon Agidigbo FM da ke Ibadan, wanda ya kasance abokin hulɗa na kafafen yada labarai.

A cewar ‘yan sanda, sauran wadanda aka kama sun hada da Genesis Christopher, mai shekaru 24; da Tanimowo Moruf, mai shekaru 52; sai Anisolaja Olabode, 42; da Idowu Ibrahim, 35; da kuma Abiola Oluwatimilehin, mai shekaru 25.

Mutane 35 ne suka mutu a turmutsutsun birnin Ibadan

EFCC tayi sammacin shugabannin kananan hukumomin da aka sauke a jihar Edo

Keeping kids in adult cells, societal time bomb – Group