Hukumar NAFDAC mai kula da inganci abinci da magunguna ta rufe kasuwar Eziukwu da ke birnin Aba a jihar Abia, bayan gano kayayyakin da suka lalace na kimanin naira milyan dubu biyar.
A sanarwar da ta wallafa jiya Laraba, hukumar ta ce an rufe shaguna dari da hamsin a kasuwar, bayan shafe kwana biyu ana samame a cikinta.
Tawagar jami’an NAFDAC ta bankado manyan wuraren samarwa da raba kayan jabu, da wadanda lokacin amfaninsu ya ƙare.
Daraktan shiyyar kudu maso gabas na hukumar, Dokta Martins Iluyomade, ya nuna takaicin yadda ake ci gaba da hada-hada ba bisa ka’ida ba, duk da matakin da shugabannin kasuwar suka sanyawa hannu a baya a watan Disambar bara na bankado masu yin jabun.
Shugabar hukumar NAFDAC, Farfesa Mojisola Adeyeye, ta tabbatar da cewa, hukumar ba za ta lamunci irin wannan dabi’a ba, inda ta jaddada ƙudurin kare lafiyar al’umma, tare da ƙoƙarin ganin an magance matsalar samar da jabun kayan da ake fama da ita a kasuwanni.
NAFDAC ta rufe kasuwa a Aba bayan gano lalatattun kayayyaki