Hukumar Kula da Abinci da Magunguna ta Kasa (NAFDAC) ta shawarci ‘yan Najeriya da su rika sayen kaya daga wuraren da za su iya bin diddigin mai sayarwa ta hanyar samun takardar shaidar siye (receipt).
Shugabar Hukumar, Farfesa Mojisola Adeyeye, ta bayar da wannan shawara yayin wata hira da ta yi da kamfanin dillacin labarai na kasa NAN a Abuja.
Ta ce sayen kaya daga wuraren da ake bayar da takardar shaidar siye zai baiwa masu saye damar bin diddigin wurin siyan kayan idan sun kasance da matsala.
Ta kara da cewa: “Idan ba a bayar da takardar shaidar siye ba, kada ka saya, saboda za ka iya fadawa tarkon kayan da ba su da inganci ko wadanda suka lalace.
“Amma idan kana da takardar shaidar siye a hannunka, za ka iya dawowa da kayan cikin sauki a kuma mayar maka da kudinka.”
Haka zalika, shugabar NAFDAC ta shawarci ‘yan Najeriya da su tabbatar da cewa duk kayan da za su saya suna da lambar rijista ta NAFDAC kafin su saya.
Adeyeye ta jaddada cewa ‘yan Najeriya su duba ranar da aka kera kaya, ranar karewar su, da kuma binciken yadda kayan suka kasance kafin su biya kudi, tana mai cewa NAFDAC tana aiki tukuru don samun al’umma mai lafiya.
Ta ce: “Tabbatar da cewa kayan da za ka saya suna da lambar rijista ta NAFDAC, ka duba da kyau, idan kayan ba su yi kyau ba, don Allah kada ka saya.
“Haka kuma, ka kula da ranar karewar kayan; kada ka saya saboda farashin kayan ya yi sauki.”
Ta kuma shawarci ‘yan Najeriya da su rika dafa abincinsu sosai, musamman hatsi, don kashe kwayoyin cuta da ka iya kasancewa a cikinsu.
NAFDAC ta shawarci al’umma su dinga karbar rasit idan sun sayi kaya