in

NNPP ta buƙaci Sufeto Janar na ‘yan sanda ya takawa kokarin kama jami’in gwamnatin Kano birki

Jam’iyyar NNPP ta yi Allah-wadai da ci gaba da ƙoƙarin kama Malam Sanusi Bature Dawakin-Tofa, Darakta-Janar na harkokin yada labarai na gwamnatin jihar Kano.

A wata sanarwa da Kakakin NNPP na ƙasa, Ladipo Johnson, ya fitar, ya bayyana cewa ‘yan sanda, bisa umarnin da suka karɓa daga Abuja, na ci gaba da ƙoƙarin kama Sanusi Dawakin-Tofa duk da umarnin kotu da ke hana daukar wannan matakin.

Ana danganta koƙarin kama Dawakin-Tofa, wanda ya haɗa har da yiwuwar barazana ga iyalinsa, ana da ƙorafi da ake zargin tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje, kuma Shugaban jam’iyyar APC ko wasu mutane da ke wakiltarsa, suka shigar.

Kakakin NNPP ya soki matakin ‘yan sanda, yana mai bayyana shi a matsayin take dokar ƙasa da kuma amfani da iko ba bisa ƙa’ida ba.

Ya ce, Sanusi ya shiga ƴar ɓuya domin kauce wa kamun da ba bisa doka ba.

“Kamar yadda jama’a za su iya gani, al’amuran Kano suna dada tabarbarewa sakamakon irin wannan amfani da iko ba bisa ƙa’ida ba, barazana da tsoratar da jami’an gwamnati,” in ji shi.

NNPP ta yi kira ga Sufeto-Janar na ‘Yan Sanda, Kayode Egbetokun, wanda aka san shi da kwarewa, da ya tabbatar cewa rundunar ‘yan sanda ta kauce wa shiga siyasar son kai.

NNPP ta buƙaci Sufeto Janar na ‘yan sanda ya takawa kokarin kama jami’in gwamnatin Kano birki

‘We’ll use peace, artificial intelligence to defeat troublemakers’ – Gov Fubara

President Tinubu redeploys 11 permanent secretaries