in

PDP ta bukaci Majalisar Dokoki da tayi watsi da kasafin kudin 2025

Jam’iyyar PDP tayi watsi da kasafin kudin tarayya na Naira tiriliyan 47.9 na shekarar 2025 da Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya gabatar a ranar laraba.

Jam’iyyar tana mai bayyana shi a matsayin “wanda ba zai yiwu ba, ba gaskiya ba, kuma cike da rashin bayyana gaskiya.”

A cikin wata sanarwa da Sakataren Yada Labarai na Kasa na PDP, Debo Ologunagba, ya fitar a ranar Laraba, jam’iyyar ta bayyana kasafin a matsayin wanda akayi ba don al’umma ba, tare da gargadin cewa aiwatar da shi zai kara tsananta matsalolin tsaro, talauci, da takaici a fadin kasa.

DailyPost ta rawaito cewa Tinubu ya gabatar da kasafin kudin 2025 ga yan Majalisar Dokokin Kasa, inda ya ware Naira tiriliyan 4.91 ga bangaren tsaro, Naira tiriliyan 4.06 don inganta ababen more rayuwa, Naira tiriliyan 2.48 ga bangaren kiwon lafiya, da Naira tiriliyan 3.52 don ilimi.

Jam’iyyar PDP tayi suka kan kasafin, tana zargin cewa ya cika da alkaluman tattalin arziki marasa tabbaci da alkawuran da ba su da tushe ko makama.

“Kasafin Naira tiriliyan 47.9 na tarayya na shekarar 2025 kasafi ne mai cin amanar al’umma, wanda idan aka aiwatar dashi, zai kara jefa kasa cikin matsalolin tsaro, talauci, da rashin fata,” in ji sanarwar.

Jam’iyyar PDP ta zargi gwamnatin Tinubu da rashin zuba jari mai ma’ana a bangarorin da suka hada da noma, wutar lantarki, man fetur, da kananan da matsakaitan masana’antu. Ta bayyana cewa wadannan bangarori ne tushen bunkasa tattalin arziki da tabbatar da kwanciyar hankali.

Haka kuma, PDP ta soki kasafin saboda rashin fayyace bayanai, musamman kan yadda za a raba kudade tsakanin ayyukan ci gaba da na yau da kullum.

PDP tayi kira ga Majalisar Dokoki ta Kasa da tayi watsi da kasafin kudin 2025 a yadda yake, tana amfani da ikon da doka ta bata don sake fasalta kasafin yadda zai mayar da hankali kan bunkasar tattalin arziki da jin dadin al’umma.

PDP ta bukaci Majalisar Dokoki da tayi watsi da kasafin kudin 2025

EPL: He has gone backwards under Arteta – Paul Scholes on Arsenal star

Ooni’s ex-wife, others in trouble over alleged sponsorship of Ibadan funfair as 32 children die