in

Shugaba Tinubu yi jimamin mutuwar yara 35 a Ibadan

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana matukar bakin cikinsa kan mummunan hadarin da ya auku a wurin wasan yara a Ibadan, wanda ya yi sanadin rasa rayukan yara 35 da raunata wasu da dama.

Shugaban ya mika ta’aziyyarsa ga gwamnatin jihar Oyo da al’ummar jihar baki daya, tare da iyalan da suka rasa ‘ya’yansu a wannan mummunan lamari.

Shugaban ya nuna jimaminsa a cikin sanarwar da mai ba shi shawara a kan kafafen yada labarai, Bayo Onanuga ya fitar.

“A cikin wannan lokaci na juyayi, Shugaba Tinubu ya bayyana goyon bayansa ga iyalan da abin ya shafa tare da addu’ar samun kwanciyar rai ga wadanda suka rasa rayukansu,” inji sanarwar.

Shugaban kasa ya ba da umarnin gaggawa ga hukumomin da suka dace da su gudanar da cikakken bincike kan musabbabin wannan bala’i.

Haka zalika, Shugaba Tinubu ya yi kira ga gwamnatin jihar Oyo da ta dauki dukkan matakan da suka dace don hana irin wannan sake faruwa.

“Lafiyar yara da jin dadinsu ya fi komai muhimmanci. Babu wani taro da ya kamata ya yi barazana ga rayuwarsu ko ya zo kafin tsaron su,” in ji Shugaba Tinubu.

Shugaba Tinubu yi jimamin mutuwar yara 35 a Ibadan

Keeping kids in adult cells, societal time bomb – Group

Okpebholo panel alleges massive fraud in execution of projects by Obaseki govt