Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kaduna ta tabbatar da cafke wasu gungun ‘yan fashin daji da suka shahara a jihar.
A cewar rahoton mai magana da yawun rundunar, wanda aka bayyana sunan wanda ake zargin a matsayin Aliyu Umar, wani matashi mai shekaru 22, an kama shi da bindigogi kirar AK 47 guda biyu tare da harsasai 50.
Wata sanarwa da rundunar ta fitar, a Alhamis din nan tace “A ranar 16 ga Disamba, da misalin karfe 6:00 na safe, jami’an sashin yaki da satar mutane, karkashin jagorancin jami’in da ke kula da sashin, SP Sani Ibrahim, sun sami bayanan sirri, wanda ya kai ga nasarar kama matashin Aliyu Umar, a Zariya,”
Bayan bincike, Umar ya amsa laifin aikata fashi da makami, inda ya bayyana cewa shi memba ne na wata kungiyar ‘yan fashin daji a Zamfara, kuma ya tafi Barikin Ladi, Jos, don karɓar makamai daga wani abokin aikinsa, wanda har yanzu ba a bayyana sunansa ba.
A wani bangare daban, ‘yan sanda sun kama wasu matafiya uku da ake zargi da satar mota, yayin da suke kokarin sayar da motar da aka sace.
Sun amsa cewa sun sace motar ne daga wani gida a Naval Quarters, Asokoro, Abuja.
“A ranar 16 ga Disamba, 2024, bayan samun sahihan bayanai cewa wasu matasa suna kokarin sayar da mota a cikin yanayi mai zargin,” in ji sanarwar.
Yan sanda a Kaduna sun kama gungun masu laifi