Rundunar ƴan sandan kasar nan ta ja kunnen masu zagin wasu a kafafen sada zumunta.
Kakakin rundunar ƴan sandan Najeriya, Olumuyiwa Adejobi, ya bayyana cewa zagin mutane ta kafafen sadarwa laifi ne a ƙarƙashin dokokin Najeriya.
Ya ce laifin zai iya kai a gurfanar da duk wanda aka samu da aikata hakan.
Adejobi ya yi wannan bayani ne ta shafinsa na X, inda ya ce: “Zagi ta kafafen sadarwa ba wani abu ne da za a ɗauka matsayin ‘yancin fadar albarkacin baki ba.
“Cin zarafi ta kafafen sadarwa ya bambanta da batanci, amma dukkansu suna zama laifi mai girma, wanda zai iya jawo hukunci. Ya kamata kowa ya kasance mai taka-tsantsan.”
Babban laifi ne ka zagi mutum a kafar sada zumunta – Yan Sanda