in

Bakuwar cuta ta bulla a Kano

Karamar hukumar Rogo ta dauki kwararan matakai don magance barkewar wata bakuwar cuta da ba a tantance ba, wadda ta shafi mazauna Yankin Kwanar Alo dake a Mazabar Ruwan Bago da wasu yankunan Karamar Hukumar.

Jami’in yada labarai na karamar hukumar Rogo, Abdu Bako Abdullahi ya bayyana haka a sanarwar da ya raba ga manema labarai a ranar Juma’a.

Sanarwar ta ce karamar Hukumar ta siyo magunguna na miliyoyin Naira domin dakile yaduwar cutar.

Shugaban Karamar Hukumar, Alhaji Abubakar Mustapha Rogo, ya jaddada mahimmancin daukar matakan gaggawa wajen magance wannan matsala kafin ta tumbatsa.

Ya umarci Shugaban Sashen Kula da Lafiya a matakin Farko da ya binciki cutar tare da daukar matakan dakile yaduwarta a fadin yankin Karamar Hukumar.

Alhaji Abubakar Mustapha Rogo ya tabbatar da cewa, karamar hukumar za ta cigaba da yin aiki kafada da kafada tare da gwamnatin Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf wajen fifita ayyukan kula da lafiya a yankin.

Ya kuma sanar da shirin gudanar da gangamin wayar da kai ga al’ummar yankin a wannan lokacin na sanyi wajen kiyayewa da yadda za ayi amfani da wuta ta hanyar jin dumi da kuma hurata domin wasu ayyuka daban.

Bakuwar cuta ta bulla a Kano

Yuletide: NSCDC deploys 28,300 personnel across Nigeria

Ex-boxing world champion Thierry Jacob dies at 59