in

Bikin krisimeti: NSCDC ta tura jami’ai 1,850 don tabbatar da tsaro a Kogi

Hukumar Tsaro ta Civil Defence ta Najeriya (NSCDC) ta tura jami’ai 1,850 domin tabbatar da tsaro a yayin murnar Kirsimeti a Jihar Kogi.

Wata sanarwa da Jami’in Hulda da Jama’a na rundunar, Abdullahi Aliyu, yasa hannu a ranar Juma’a, ta bayyana cewa, Kwamandan NSCDC na Jihar Kogi, Esther Akinlade, ta zabi wadannan jami’ai daga sassa daban-daban na hukumar, ciki har da sashen Ayyuka, Mata, da kuma sashen Tsaro na Kayan Aikin Kasa.

Kwamanda Akinlade ta yi kira ga matasa da su kaurace wa duk wani hali na rashin da’a ko aikata ayyukan da ba su dace ba, wadanda za su iya haifar da rashin doka da tsaro, domin duk wanda aka kama zai fuskanci hukuncin doka.

“Ta kuma yi kira ga jama’a dasu gudanar da bukukuwan Kirsimeti cikin nutsuwa, tare da bada rahoton duk wata sahihiyar bayanai game da ayyukan laifi ko maboyar masu laifi ga hukuma, domin taimakawa wajen tabbatar da zaman lafiya a jihar,” in ji sanarwar.

Bikin krisimeti: NSCDC ta tura jami’ai 1,850 don tabbatar da tsaro a Kogi

Tinubu ya bukaci a gudanar da bincike kan turmutsitsin Ibadan

Sexyy Red: Bana daukar aure da muhimmanci saboda cin amanar maza