Tsohon Kakakin Majalisar Wakilai ta 9, Yakubu Dogara, ya danganta koma bayan yankin Arewa da halin da shugabanninta suka jefa yankin a ciki.
Haka kuma, ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su mara wa Shugaba Bola Tinubu baya wajen sauya fasalin kasar ta hanyar gyaran dokokin haraji da ke jiran amincewar Majalisar Kasa.
Dogara ya yi wannan jawabi ne a matsayin babban bako mai jawabi a wani taron tattaunawa da shugabannin Kiristoci na Arewa.
Taken taron shi ne: “Coci da Al’umma: Gyaran Haraji da Matsalolin da Ke Tafe,” inda aka tattauna batutuwan da suka shafi mulki da cigaban kasa.
Dogara ya koka kan yadda shugabannin siyasar Arewa suka yi sakaci da damar jagorantar Najeriya na tsawon shekaru 40, inda suka bar yankin cikin talauci da koma baya.
A cewarsa, ya zama dole ‘yan Arewa su guji zargin Shugaba Tinubu game da halin da yankin Arewa ke ciki a halin yanzu. Ya yi kira ga al’ummar yankin da su hada kai wajen mara wa kudirin dokokin gyaran haraji baya, wadanda ya ce za su kawo sauyi ga Arewa da Najeriya baki ɗaya.
“Dukkanmu ‘yan Arewa ne, kuma ya kamata a fahimci cewa Shugaba Tinubu ko kudu ba su zama matsalar Arewa ba. Ba su zo domin cutar da Arewa ba. Wannan ba gaskiya ba ne. Wasu na zargin cewa ‘yan kabilar Yarbawa na samun mukamai, amma bari mu yi nazari. Mun yi mulki a wannan kasa na tsawon sama da shekaru 40 lokacin da ‘yan Arewa ke kan mulki. Me muka cimma? Arewa ta kasance yadda take, a talauce, sanadiyyar shugabanninmu,” in ji Dogara.
Da yake magana kan Harajin Kayayyaki (VAT) da rabon kudaden tarayya da jihohi ke samu, Dogara ya tambaya: “Mun samu kudade masu yawa, amma me gwamnatocinmu suka yi da su? Sun yi almubazzaranci da su maimakon saka su a ayyukan cigaba masu ma’ana.”
Ya kuma ambaci masana’antar karafa ta Ajaokuta, wadda gwamnatin Shagari ta kaddamar, wanda aka kammala kashi 98 cikin 100 amma aka bari ta lalace.
Dogara ya yi kira ga ‘yan Arewa da su mara wa kokarin Shugaba Tinubu na sauya fasalin kasa ta hanyar dokokin gyaran haraji da ke gaban Majalisar Dokoki ta Kasa.
Dogara ya caccaki shugabannin Arewa