in

Gwamnan Kano ya halarci daurin ‘yar gwamnan Jigawa

Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya halarci daurin auren ‘yar gwamnan jihar Jigawa Dr. Salma Umar Namadi Danmodi da angonta Abba Sulaiman Musa.

Gwamna Abba Kabir Yusuf yayi addu’ar Allah ya albarkaci auran ya basu zaman lafiya Mai dorewa tare da zuri’a mai albarka.

A nasa bangaren mai masaukin baki, gwamnan jihar Jigawa Mal. Umar Namadi ya godewa mahalarta taron, tare da addu’ar Allah ya maida kowa gidansa lafiya.

Taron daurin auren wanda ya gudana a babban masallacin juma’a na garin Dutse ya samu halartar gwamnonin Katsina da Gombe da Yobe da kuma karamar ministar ilimi Hajiya Suwaiba Sa’ad Ahmad da sauran manyan baki daga ciki da wajen jihar Jigawa.

Gwamnan Kano ya halarci daurin ‘yar gwamnan Jigawa

Review curriculum to reduce Japa syndrome – Lecturer tells Nigerian Govt

Land revocation: Speaker Abbas not owing FCTA – Aide