A ranar Litinin, ɗan wasan gaba na Super Eagles, Ademola Lookman, ya bi sahun Victor Osimhen ta hanyar lashe kyautar Gwarzon Ɗan Kwallon Afrika na CAF.
Bayan wannan nasara, wasu ‘yan wasan Super Eagles kamar William Troost-Ekong, Frank Onyeka, Victor Boniface, da wasu da dama sun yi amfani da kafafen sada zumunta domin taya shi murna.
Amma Osimhen bai ce komai ba tun bayan da Lookman ya ci wannan kyauta.
Abubuwan da yake wallafawa a shafukansa na sada zumunta kawai hotunan kansa ne a cikin kayan alfarma na Louis Vuitton.
Wani mai bibiyar sa ya ƙara hura wutar zancen, inda yace: “Al’umma na cewa baka taya Lookman murna ba.”
Osimhen ya mayar da martani cikin sauri: “Suna ta abinsu ba su sani ba cewa na taya shi murna nan da nan bayan wasanmu.”
Amma dai har zuwa lokacin da ake wannan rahoto, bai taya Lookman murna ba.
Gwarzon CAF: Har yanzu Osimhen bai taya Lukman murna ba