Wata babbar kotun jiha da ke zama a Fatakwal, babban birnin Jihar Ribas, ta soke zabukan mazabu, kananan hukumomi, da jiha na jam’iyyar APC a jihar karkashin jagorancin Tony Okocha a matsayin shugaban jam’iyyar.
Alkalin da ya jagoranci zaman, Mai Shari’a Godswill Ogbomanu, ya yanke hukuncin a ranar Juma’a, inda ya soke zabukan jam’iyyar bisa la’akari da umarnin kotu da ya hana jam’iyyar ci gaba da gudanar da zaben.
Haka kuma, kotun ta ci tarar APC naira miliyan goma (₦10,000,000).
Da yake martani, lauyam masu kara, Emenike Ebette, ya yaba da hukuncin kotun, yana bayyana shi a matsayin adalci ga masu karar.
“Adalci ya yi aiki saboda an yi musu rashin gaskiya. Idan akwai wani lamari a gaban kotu kuma kotu ta ce kada a yi abin, amma sai ka ci gaba da yin hakan, rashin kunya ne,” in ji shi.
A nasa bangaren, lauya wadanda aka yi kata, William Wobodo, ya ce za su sanar da kwamitin gudanarwa na kasa na jam’iyyar APC game da hukuncin kotu kafin yanke mataki na gaba.
Kotu ta soke zaben APC a Ribas