in

Kungiyar hada kan Arewa tayi watsi da rahoton hukumar kiddiga ta kasa

Kungiyar hada kan Arewa (CNG) ta yi Allah-wadai da sabbin rahotannin da Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) ta fitar kwanan nan.

A ranar 17 ga Disamba, NBS ta bayyana cewa ‘yan Najeriya sun biya jimillar Naira tiriliyan 2.23 a matsayin kudin fansa daga watan Mayun 2023 zuwa Afrilun 2024.

Hukumar ta kuma fitar da rahoton binciken ƙididdigar laifuka da hangen nesa kan tsaro, wanda ya nuna cewa kimanin laifuka miliyan 51.89 sun faru a lokacin da aka yi nazarin.

A martanin kungiyar CNG ta bakin Kwamared Jamilu Aliyu Charanchi, shugabanta na Kasa, ta ce babu gaskiya a rahoton, tare da nuna bambancin ga Arewa a matsayin yanki mai fama da matsalolin tsaro marasa magani.

CNG ta yi tantamar sahihancin rahoton, tana mai cewa “ba a bayyana tsarin nazarin yadda ya kamata ba, wanda hakan ya haifar da tambayoyi kan bayanan.”

Kungiyar ta ce adadin da aka bayar, musamman dangane da yankunan Arewa maso Yamma da Arewa maso Gabas, sun yi yawa sosai kuma ba daidaito da hakikanin yanayin da yankunan ke ciki.

“inda aka samu cigaba wajen inganta tsaro, makonni kadan da suka gabata sojojin Najeriya suka rusa sansanoni 22 na ‘yan ta’addan Lakurawa a jihohin Kebbi da Sakkwato.”

Kungiyar hada kan Arewa tayi watsi da rahoton hukumar kiddiga ta kasa

Dogara ya caccaki shugabannin Arewa

Gov Idris swears four new high court judges in Kebbi