in

Majalisar wakilai zata mika kudin da ta rage daga albashinsu ga shugaba Tinubu

Majalisar Wakilai ta ce za ta gabatar wa shugaban kasa Bola Tinubu kuɗin da suka tara daga albashinsu domin ba da tasu gudummawar wajen rage wa ‘yan Najeriya raɗaɗin tsadar rayuwa.

Kakakin Majalisa Tajudeen Abbas ne ya bayyana cewa kuɗin da suka tara sun kai naira miliyan 700 yayin zaman majalisar na ranar Alhamis din nan. Ya ce za su mika kudin a ranar 31 ga watan Disamban 2024.

Tun dai a watan Yuli ne ‘yan majalisar suka yi alƙawarin sadaukar da rabin albashinsu domin taimakawa saboda cire tallafin man fetur.

Majalisar wakilai zata mika kudin da ta rage daga albashinsu ga shugaba Tinubu

ICPC ta bankado badakalar ayyukan mazabu da darajar su yakai Naira miliyan 350

Muna dab da rasa zangon karatu saboda kasa biyan kudin makaranta – Daliban BUK