Jam’iyyar NNPP a Jihar Kano ta tabbatar da cewa tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar, Abdullahi Baffa Bichi, da kwamishinan sufuri, Muhammad Diggol, har yanzu jam’iyyar bata dage dakatarwar da tayi musu don ba’a kammala bincike kan tuhumar da ake musu.
Da yake magana da manema labarai a ranar Alhamis, Shugaban jam’iyyar a jihar, Hashim Sulaiman Dungurawa, ya ce dakatarwar na nan daram har sai an kammala binciken jam’iyyar.
Idan za’a iya tunawa NNPP ta dakatar da Bichi da Diggol bisa zargin rashin biyayya da cin amanar ofis. Da yake karin bayani kan matakin jam’iyyar, Dungurawa ya bayyana cewa jam’iyya da gwamnati bangarori ne daban.
“Jam’iyya da gwamnati bangarori ne daban kuma kowanne yana gudanar da aikinsa daban. Gwamnati ta dauki matakin da ta ga ya dace a nata bangaren, yayin da mu kuma muke yin namu binciken,” ya bayyana.
A kwanakin baya an bayyana cewa an sallami Bichi, daga mukaminsa bisa rashin lafiya tare da wasu kwamishinoni guda biyar yayin da aka chanjawa kwamishina Diggol, sabon ofis a matsayin kwamishinan kula da ayyukan gwamnati da bincike.
Shugabancin NNPP ya jaddada aniyarsa na tabbatar da bin doka da oda a cikin jam’iyya tare da barin gwamnati ta gudanar da aikinta cikin ‘yanci.
NNPP tace haryanzu an dakatar da Bichi da Diggol har sai an kammala bincike