Fitacciyar mawaƙiyar Amurka, Sexyy Red, ta bayyana cewa aure kawai wata “al’ada” ce saboda dabi’ar maza ta cin amanar mata da yaudara.
Mawaƙiyar da ta shahara da waƙar ‘Rich Baby Daddy’, Sexyy Red, tace za tayi aure amma ba za ta taɓa aminta da abokin zamanta ba.
Ta bayyana cewa tana da yakinin cewa duk maza suna da cin amana.
A wata hira da tayi kwanan nan da Angel Reese, Red ta ce, “Zan yi aure amma ina ganin cewa aure kawai yaudara ne. Ina ganin duk maza suna cin amana.”
“Ko dabana soyayya, nasan maza suna cin amana. Shi yasa ban da wani fata. Ban taɓa haɗuwa da wani namiji da baya cin amana ba.
“Ko da namiji yace min ba zai ci amana ta ba, ba zan yarda ba. Za mu iya yin aure, amma a ƙarshe, kawai al’ada ce. Banzan yarda da na miji ba.”
Sexyy Red: Bana daukar aure da muhimmanci saboda cin amanar maza