in

CBN ya umarci bankuna su cika na’urar ATM da kudi

Babban banki kasa (CBN), ya umarci bankuna da su sanya isasshen kudi a na’urar cirar kudi ta ATM dake dukkanin rassansu.

Wannan dai wani yunkuri ne na magance matsalar karancin takardun kudi da al’umma ke kuka da ita a ‘yan kwanakin nan.

Takardar umarnin mai kwanan watan 29 ga watan Nuwanba, 2024 da mukaddashin darakatn kudi na bankin, Solaja Olayemi da darakta mai kula da rassan bankuna, Isa Olatinwo Aisha suka sanyawa hannu, ta zayyana matakan da za a bi wajen warware matsalar karancin kudi.

Bankin ya kuma bada tabbacin bin diddigin yadda bankuna zasu yi aiki da wannan umarni.

Yan Najeriya da dama na kokawa saboda yadda ake cigaba da samun karancin takardun kudi musamman ma kanana, irin su N20, N50, N100 da kuma N200.

A jihar Kano masu kananan sana’oi da DAILY POST HAUSA ta tattauna dasu sun ce kasuwancinsu ya samu koma baya saboda karancin kudi a hannun mutane.

CBN ya umarci bankuna su cika na’urar ATM da kudi

Yan wasan Kano Pillars 3 zasu bugawa Najeriya wasa

Okpebholo appoints Anthonia Njoku Chief Medical Director Edo Specialist Hospital