Reshen Kano na kungiyar mata lauyoyi ta duniya, ya gudanar da gangamin wayar da kan jama’a illar cin zarafin mata, a wani bangare na makon yaki da cin zarafin `ya’ya mata na duniya.
A tataunawarta da manema labarai a ranar Laraba, shugabar kungiyar a Kano, Bilkisu Ibrahin Suleman ta bayyana cewa cin zarafi ba wai ya tsaya ne kawai a fyade ba, wata matsala ce da kan dabaibaye iyali, dama al’umma baki daya.
Inda tace akan ya samu a gidaje ko unguwa ko makarantu ko wuraren aiki da sauransu.
Ta kuma bayyana illolin da yake haifarwa da suka hada da hana yara samun damar nasara a rayuwa kamar sauran mutane.
Ta yi kira ga al’umma da su hada hannu da kungiyar domin dakile karuwar matsalar, yayin da aka ba shawarwari, da taron masu ruwa da tsaki.
Taron ya kunshi kungiyoyin kare hakkin dan adam da sauran dai dai kun mutane.
Cin zarafin mata: An gudanar da gangamin wayar da kai