A taron tunawa da ranar yaki da cin hanci da rashawa ta duniya na shekarar 2024, shugaban hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC, Mista Ola Olukoyede, ya bukaci matasan Najeriya da su hada kai wajen yaki da cin hanci da rashawa.
Olukoyede ya bayyana wannan ne a ranar Alhamis yayin taron tattaunawa da al’umma da ofishin EFCC na Kano ya shirya, domin bikin Ranar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Duniya.
Ibrahim Shazali daraktan hukumar EFCC, anan Kano wanda ya wakilci Olukoyede ya jaddada bukatar matasa su hada kai domin yaki da cin hanci da rashawa, wanda ya bayyana a matsayin wani dodo da ya shafi kowane rukunin shekaru, amman yafi shafar matasa.
Olukoyede ya ci gaba da cewa, domin samun hadin kai wajen yaki da cin hanci da rashawa, ya kamata matasa su kafa kungiyoyi, da kuma al’ummomi masu inganta kyawawan dabi’u.
Ya kuma kara musu kwarin guiwa da su bada goyon baya ga hukumomin yaki da cin hanci da rashawa kamar EFCC da kuma bankado ayyukan cin hanci da rashawa a yankunansu.
Ku guji cin hanci da rashawa – Shugaban Hukumar EFCC ya shawarci matasa