Rundunar sojin Najeriya ta ce ta yi nasara wajen kashe ƴan ta’dda 8,034 a cikin shekarar 2024 da za ta kara a watan nan.
Rundunar ta kuma ce an kama wasu ‘ƴan ta’dda’ 11,263 da kuma ceto mutum 6,376 da aka yi garkuwa da su.
Wannan na kunshe a cikin sanarar da kakakin rundunar, Manjo-janar Edward Buba ya fitar.
Sanarwar ta bayyana cewa an samu nasarar ne a samame daban-daban da sojoji suka kai yankunan Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma da Arewa maso Tsakiya da sauran shiyyoyi.
“Mun kuma samu nasarar ƙwato makamai 8,216 da harsasai 211,459. Mun kuma daƙile yunkurin satar ɗanyen mai da kuɗinsa ya kai sama da naira biliyan 57,” in ji Buba.
Sojoji sun hallaka yan ta’adda sama da 8,000 a 2024