SHARE

Waleed Abdullah, tsohon mai tsaron ragar ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Saudiya, Al-Nassr, ya yi ikirarin cewa fitaccen ɗan ƙwallon ƙafa ƙasar Portugal, Cristiano Ronaldo, yana sha’awar shiga addinin Musulunci.

Da yake magana a wani shirin talabijin, Abdullah, wanda ya buga wa Al-Nassr wasa daga 2017 zuwa 2024, ya bayyana cewa Ronaldo yana girmama addinin Musulunci ta hanyoyi daban-daban, yana nuna sha’awarsa ga wannan addini.

“Ronaldo yana son ya zama Musulmi. Na yi magana da shi game da haka, kuma ya nuna sha’awa,” in ji Abdullah. “Ya riga ya taɓa yin sujada a fili bayan zura ƙwallo, kuma koyaushe yana ƙarfafar ‘yan wasa su yi sallah da sauran ayyukan ibadah.”

Abdullah ya kuma ce tauraron Al-Nassr yana tabbatar da cewa abokan wasansa suna da isasshen lokaci don yin sallolinsu yayin daukan horo. Ya ce Ronaldo yana da sha’awar koyon al’adun Saudiya tun lokacin da ya iso ƙasar a karon farko.

Ya lura cewa idan aka yi kiran salla yayin horo, Ronaldo kan roƙi da a dakatar da daukam horon har sai an gama salla.

“A farkon, na kasance kusa da Cristiano saboda bai saba da al’adun ƙasar, ƙungiyar, ko sauran abubuwa ba. Yana da sha’awa kuma sau da yawa yana tambayata tambayoyi game da wasu abubuwa,” in ji Waleed.

Christiano Ronaldo ya fada min yana so ya musulunta – Abdullahi

NO COMMENTS