Kungiyar Arewa Consultative Forum (ACF) ta Jihar Kano ta yi murna da cikar shekaru 99 na Alhaji Tanko Yakasai.
Alhaji Yakasai ya shahara wajen bada gudunmawa a harkokin siyasa da ci gaban yankin Arewa.
A cikin wata sanarwa da Sakataren Yada Labaran ACF, Alhaji Bello Sani Galadanchi, ya fitar ranar Alhamis, kungiyar ta yabawa Alhaji Tanko Yakasai bisa gagarumar gudunmawarsa wajen yaki don samun ‘yancin kai da cin gashin kansa na Najeriya.
Sanarwar ta kuma nuna cewa Yakasai na daga cikin manyan ‘yan Najeriya da suka yi fafutukar samun ‘yancin kasar.
ACF ta kuma yabawa gudunmawar Alhaji Tanko Yakasai a fannin ci gaban al’umma, kafa jihar da kuma inganta zaman lafiya a tsakanin al’ummomin Najeriya masu banbancin kabila da addini.
Kungiyar ta nuna cewa Yakasai ya taka muhimmiyar rawa wajen samar da hadin kai da zaman lafiya a cikin kasar.
Shugaban ACF na Jihar Kano, Dr. Goni Umar, ya bayyana farin cikinsa da murnar cikar shekaru 99 na Alhaji Tanko Yakasai.
Ya taya al’ummar Kano da iyalan Yakasai murnar wannan gagarumin lamari.
Dr. Umar ya yi addu’ar ci gaba da albarkar ayyukan Yakasai a matsayin mai fafutukar al’umma, dan kasuwa, mai kawo zaman lafiya, da mai sharhi a harkokin jama’a.
ACF ta taya Tanko Yakasai murnar cikar shekaru 99