Ma’aikatar lafiya ta jihar kano zata fara tarawa gwamnati kuɗin haraji a shekarar 2025 wanda hakan zai ƙara habbaka tattalin arzikin jihar.
Kwamishinan lafiya na jihar Dakta Abubakar Labaran Yusuf ne ya bayyana hakan jim kaɗan bayan kammala kare kasafin kuɗin ma’aikatar a zauren majalisa.
Kwamishinan ya ce a wannan shekarar mai kamawa ta 2025 ma’aikatar ta lafiya zata fara tarawa gwamnati kuɗin haraji domin a ɓangaren Asibitoci akwai ɓangaren da za’a iya samarwa da gwamnati wasu kuɗaɗe.
Haka zalika Kwamishinan yace ma’aikatar tasa ta shirya daukar sabbin ma’aikatan kula da harkar lafiya a faɗin jihar kano.
Yace a wannan lokaci duk wani aiki da aka fara ba’a kammala ba a fannin harkar lafiya za’a tabbatar da an kammala shi.
Ma’aikatar lafiya ta jihar Kano zata fara tarawa gwamnati Haraji a 2025