SHARE

Hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC reshen jihar Kano ta bukaci matasa su himmatu wajen taimakawa duk wani shiri na yaki da cin hanci da rashawa a kasar.

Kwamandan shiyya na hukumar Ibrahim Shazali ne yayi wannan kira a taron masu ruwa da tsaki kan yaki da rashawa a shirye shiryen bikin ranar yaki da cin hanci da rashawa ta duniya da ake gudanarwa ranar 9 ga watan disambar kowacce shekara.

Ibrahim Shazali ya ce a wannan shekara an yi duba ne kan irin rawar da matasa za su taka wajen yaki da cin hanci a tsakanin al’umma.

Shima da yake jawabi a wajen taron shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano Muhyi Magaji Rimingado ya ce an tattauna batutuwa da za su taimaka wajen samun nasarar yaki da cin hanci.

Taron ya samu halartar hukumar ICPC, hukumar wayar da kan al’umma NOA, kungiyar yan jaridu,kungiyoyin fararen hula da sauransu.

EFCC ta bukaci matasa su tallafawa yaƙi da cin hanci da rashawa

NO COMMENTS