SHARE

Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Ibrahim Shekarau, tare da wasu manyan mambobin kungiya mai rajin farfado da ruhin dmokuradiyyar a Arewa, sun ce an da kafa kwamitin don sake duba kudirin na gyaran haraji da ke gaban majalisar kasa.

An bayyana wannan matakin ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun kungiyar LND, Ladan Salihu, ya fitar a Abuja.

Salihu ya bayyana cewa kungiyar LND za ta binciki kudirin ne biyo bayan cece-kuce da zarge-zargen da suka biyo bayan gabatar da kudirin.

Mai magana da yawun kungiyar ya bayyana mambobin kwamitin da za su binciki kudirin a matsayin kwararru daga Arewa a fannonin shari’a, ilimin kudi da sauransu, inda ya ce an ba su mako guda don kammala cikakken nazarin kudirin.

“Bayan kammala aikinta, kwamitin zai gabatar da sakamakonsa ga jama’a.”

“Kungiyar LND tana tabbatar wa jama’a  cewa yan kwamitin sun kware kuma za su samar da shawarwarin da su ka dace,” in ji sanarwar.

Yan siyasar Arewa za su nazarci kudirin dokar haraji

NO COMMENTS