SHARE

Shugaban Jamus, Dr. Frank-Walter Steinmeier, zai kawo ziyarar kwanaki uku zuwa Najeriya, daga ranar 10 zuwa 12 ga watan Disamba.

Wannan ziyara ita ce karo na uku da manyan shugabanni daga kasashen biyu ke kaiwa juna, tun bayan rantsar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu a watan Mayu 2023.

A lokacin ziyarar, Shugaba Steinmeier zai kasance tare da wata tawaga ta manyan shugabannin masana’antu da mambobin kwamitocin kamfanoni yan kasuwa daga Jamus, wadanda ke aiki a fannin fasahar sadarwa (IT), fasahar zamani, da kuma makamashi.

An dai tsara Shugaba Steinmeier zai gana da manyan shugabannin kaaar nan, ciki har da Shugaba Tinubu da kuma Dr. Alieu Omar Touray, Shugaban Kungiyar Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka (ECOWAS).

Baya ga tarurrukansa da hukumomi a Abuja, Shugaba Steinmeier zai kuma ziyarci Legas, inda zai gana da mashahuran masu fasaha na Najeriya, ciki har da Dr. Nike Okundaye, wadda aka fi sani da Mama Nike mai kamfanin Nike Art Gallery, da kuma wanda ya lashe lambar yabo ta Nobel a Adabi, Farfesa Wole Soyinka.

Shugaban Jamus zai iso Najeriya ranar Talata

NO COMMENTS