Yayin da ya rage kusan makonni biyu kacal kafin bikin Kirsimeti da bukukuwan sabuwar shekara, samun takardun kudi a jihohin Kaduna, Kano da Katsina ya zama babban kalubale.
Kamfanin dillacin labarai na kasa (NAN) ya ruwaito yadda al’umma ke kuka kan wannan mawuyacin hali wanda ya tuna musu da irin shigen wannan matsala a lokacin bikin Kirsimeti na shekarar 2022 karshen gwamnatiin Muhammadu Buhari.
Mazauna yankin da ke cikin damuwa sun yi kira ga hukumomin da abin ya shafa da su dauki mataki cikin gaggawa domin kada a kawo cikas ga bikin Kirsimeti da sabuwar shekara mai zuwa.
A cikin garin Kaduna, wasu masu gudanar da sana’ar POS sun koka kan matsanancin karancin kudi yayin da bankuna ba sa ba da kudi sama da N20,000.
Wasu daga cikin masu POS din da suka tattauna da NAN sun ce sun fara fuskantar wannan karancin kudi tun watan Disambar Bara.
Adamu Amadu ya bayyana cewa yana samun kudinsa daga wani dan kasuwa ta hanyar yin canji da karamin kudi.
Haka nan, Ibrahim Nur ya ce yana baiwa abokan huldarsa da ke bukatar kudin da ba su wuce tsakanin N1,000 zuwa N10,000 kadai saboda tsananin karancin kudi.
A gefe guda kuma, wasu daga cikin masu hulda da POS sun koka kan tsadar cajin cirar kudin, baya ga wanda bankuna ke caji.
Bilkisu Moda ta bayyana cewa ta ziyarci cibiyoyin POS uku tana neman kudi, amma ba ta samu ba, sai daga bisani ta ciri kudi daga ATM bayan ta yi tafiya mai nisa.
A nata bangaren, Jamila Sani ta ce ta ciri N5,000 kuma ta biya N100 a matsayin kudin caji, wanda ta ce shine farashin da take biya a da.
A Kafanchan, mazauna garin sun bayyana takaicinsu kan wannan matsala.
Felicia Christopher, wata mai POS, ta shaida cewa wannan matsalar ta yi matukar shafar kasuwancinta.
“Karancin kudin ya yi matukar shafar kasuwancina domin ba na samun riba kamar yadda na saba.
“Bankuna ba sa bayar da kudi sama da wani adadi a rana kuma yana matukar batan rai,” in ji ta.
Wani mai POS, Sadiq Abdulazeez, ya bayyana cewa karancin kudin ya sa ya dakatar da ayyukansa na wucin gadi.
Wannan dai na faruwa ne duk da umarnin babban bankin kasa CBN na bankunan su tabbatar sun saka isasahen kudi a naurar su ta ATM a makon jiya.
Karancin tsabar kuɗi ya ƙaru a Kano da wasu jihohi